Kotun koli ta tabbatar da nasarar Ahmadu Fintiri a matsayin zababben gwamnan jihar Adamawa.
Ku tuna cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 11 ga watan Maris.
Sai dai kuma Sanata Aisha Dahiru Binani ta jam’iyyar APC ta kalubalanci nasarar tasa a gaban kotu.