Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori Yakubu Dogara daga mukaminsa na majalisar wakilai tare da bayyana kujerarsa a matsayin wadda ba kowa.
Dogara, wanda ke wakiltar mazabar Bogoro/Dass a jihar Bauchi, ya kasance kakakin majalisar wakilai tsakanin 2015 zuwa 2019.
Alkalin kotun, D.U. Okorowo, a ranar Juma’a, ya yanke hukuncin cewa, ficewar Dogara daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC kuskure ne, kuma yana nufin ya bar kujerar majalisa.
Dogara dai ya koma APC ne bayan ya sake lashe zabensa a karkashin jam’iyyar PDP a 2019.
Dangantakarsa da ta yi tsami da gwamnan jiharsa, Bala Mohammed, na daya daga cikin manyan dalilan da ya sa ya fice daga jam’iyyar PDP da ya koma kasa da shekaru biyar da suka wuce.