Kotun daukaka kara reshen Enugu, a ranar Juma’a ta kori karar da ke neman a kori Gwamna David Umahi da mataimakinsa Kelechi Igwe daga ofis, saboda sauya sheka zuwa wata jam’iyya.
A watan Nuwamba 2020 Messrs Umahi da Igwe sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Bayan sauya shekar tasu, dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamna na 2019, Sonni Ogbuoji, da mataimakinsa, Justin Mbam, sun garzaya wata babbar kotun jihar Ebonyi suna neman ta kori gwamnan da mataimakinsa.
Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta bayyana kujerar gwamna a matsayin wanda ba kowa, saboda sauya shekar mutanen biyu daga PDP zuwa APC.
Messrs Ogbuoji da Mbam sun kuma bukaci kotun da ta bayar da umarnin a rantsar da su cikin gaggawa tunda sun zo na biyu a zaben gwamna na 2019.
Amma babbar kotun da ta yanke hukunci a ranar 28 ga watan Fabrairu ta kori karar tare da bayar da Naira 500,000 a matsayin diyya ga wanda ya shigar da karar.
Ba su gamsu da hukuncin ba, masu gabatar da kara sun daukaka kara kan hukuncin.
A hukuncin da ta yanke, a ranar Juma’a, kotun daukaka kara ta amince da hukuncin da karamar kotun ta yanke kan lamarin.
ⓘ