Edith Olumide Agoye ya ajiye mukaminsa na babban kocin kungiyar Shooting Stars bayan ya shafe shekaru tara yana jagorantar kungiyar.
Agoye ya taimaka wa 3SC ta samu daukaka zuwa NPFL a kakar wasa ta 2020/21 amma sukar da magoya bayansa ke yi a kai a kai ya tilasta wa tsohon dan wasan barin mukamin.
Tsofaffin zakarun NPFL sun yi nasarar tsallake rijiya da baya a kakar wasan data gabata.
Oluyole Warlords dai sun kare ne a matsayi na 16 a kan teburi kuma sun tsallake rijiya da baya ne sakamakon samun karin kwallaye a raga da Katsina United ta 17.