Kimanin sa’o’i 24 da sace mahaifiyar dantakaar jam’iyyar APC a mazabar Kano ta tsakiya, AA Zaura, jami’an tsaro na farin kaya, DSS, sun kubutar da ita a wani wuri mai nisa a jihar Jigawa.
Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki garin Zaura da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano tare da yin garkuwa da mahaifiyar Zaura a safiyar ranar Litinin.
An yi garkuwa da Hajiya Laure Mai Kunu da misalin karfe 4 na safe kafin kiran kiran Sallar asuba. Rahotanni sun bayyana cewa an sace Hajiya Laure ne daga gidanta da ke kauyen Zaura mai tazarar kilomita biyar daga babban birnin.
Shugaban karamar hukumar Ungogo, Engr. Abdullahi Garba Ramat, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, jami’an tsaro ba su sanar da shi lamarin a hukumance ba.