Ma’aikatan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), sun fara yajin aiki, saboda rashin biyansu albashi.
Ma’aikatan da ke karkashin kungiyar ma’aikatan lafiya da ma’aikatan lafiya ta ƙasa (MHWUN), sun sanar da daukar matakin a yau Laraba.
A shekarar 2021 kungiyar ta tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai, domin neman a biya su bashin karin girma na 2018 da 2019 da suke bin mambobinta.
Da yake magana a ranar Laraba a ofishin NAFDAC da ke Legas, shugaban kungiyar na jihar, Auwalu Yusuf Kiyawa, ya ce, yajin aikin ya fara ne da gaggawa.
Kiyawa ya ce, kungiyar ba za ta janye yajin aikin ba, har sai an biya ma’aikata kudaden jin dadin su.