Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da gaggauta dawo da Najeriya gasar kwallon kwando ta duniya.
Sakataren din-din-din na ma’aikatar matasa da ci gaban wasanni ta tarayya Ismaila Abubakar ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis a wani taron manema labarai a Abuja.
A cewarsa, an amince ne biyo bayan wata takardar daukaka kara mai dauke da kwanan watan 17 ga watan Yuni, 2022, mai dauke da sa hannun Musa Kida, shugaban hukumar kwallon kwando ta Najeriya, kuma aka mikawa ministan matasa da wasanni Sunday Dare.
Abubakar ya ce, “Wasikar ta yi kira ga Ministan da ya yi amfani da ofisoshi masu kyau wajen tuntubar Shugaba Buhari, domin sauya shekar da Najeriya ta yi na janyewar Najeriya daga gasar kwallon kwando ta kasa da kasa.