Finidi George ya yi murabus daga mukaminsa na kocin Super Eagles.
Ana kyautata zaton Finidi ya dauki matakin ne a ranar Asabar kwanaki bayan da hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta sanar da daukar wani mai ba da shawara kan harkokin fasaha na kasar waje.
Tsohon jami’in yada labarai na Eagles, Toyin Ibitoye, ne ya tabbatar da ficewar sa a shafin sa na X.
Ibitoye ya rubuta: “Labarai a yanzu haka: Finidi George @FinidiGeorge_FG ya yi murabus daga mukaminsa na manajan @NGSuperEagles.”
An nada Finidi ne kawai a ranar 29 ga Afrilu, 2024, don maye gurbin Jose Peseiro, wanda kwangilarsa ta kare a watan Fabrairu.
A cikin kankanin wa’adinsa, tsohon kocin Enyimba ya jagoranci wasan da suka tashi 1-1 da Afrika ta Kudu da kuma doke su da ci 2-1 a hannun jamhuriyar Benin, duka a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.