Wani abun fashewa, a wannan karon daga wani kantin sayar da iskar gas ya kona shaguna tare da raunata mutane 20 a jihar Kano.
Lamarin na baya-bayan nan a cewar rahotanni ya afku ne a wata unguwa mai cike da cunkoso da ke unguwar Sheka, Karshen-Kwalta a cikin birnin Kano.
Gobarar ta lalata wurin da wasu shaguna kusan uku da ke kusa, ciki har da wani bangare na wani gida da ke daura da shagon.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, mutane 20 ne lamarin ya rutsa da su, amma an ceto su da ransu, kuma yanzu haka suna jinya a asibitoci.
Yusif ya ce, lamarin ya faru ne sakamakon gobarar wani mutum mai soya da sayar da kifi a kusa da shagon gas, wanda ya yi sanadiyar faruwar lamarin. In ji Blueprint.