Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta sanar da kama wasu mutane 31 da ake zargi da damfarar yanar gizo a maboyarsu a kan titin Meniru Agbani da kuma Estate Diamond, jihar Enugu.
Hukumar, a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter, ta ce, an kama wadanda ake zargin ne a ranar Talata.
An bayyana sunayensu kamar haka: Daniel Chukwuemeka, Okechukwu Chisom, John Chizoba, Benard Uguochukwu, Nwobodo Christian, Nwiba Chukwuemeka, Eze Ani Ifechukwu, Chikwe James, Emmanuel Chukwuebuka, Ezugwu Chidera, Friday Daniel, Destiny Ekene, Prosper Nnachetam, Justice Chinedu da Bright Chimezie. .
Sauran sun hada da Ezugu Nkejika, Echi Ikechukwu, Udeh Emeka, Charles Kosisochukwu, Ojinaka Smith, Ekene Chukwuebuka, Efe Samuel, Goodness Ifeanyi, Victory Anointing, Uche Egbo, Onuigbo Kingsley, Okakpu Chukwuemeka, Nnamdi Odo, Mbah Emmanuel, Collins Nweke da Jason Obi.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta ce, kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da mota kirar Mercedes Benz C400, da Toyota Corolla 2005 model guda daya, Toyota Camry, wayoyin hannu da dama, da kwamfutoci.
Ya kara da cewa, za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.