Burnley da ke fafutuka, ta kori Sean Dyche da saura wasanni takwas a yunkurin da take yi na kaucewa faduwa daga gasar Premier.
A ranar Lahadi ne Clarets za ta kara da West Ham da maki hudu tsakaninta da Everton mai matsayi na 17.
Kuma shugaban kungiyar, Alan Pace ya bayyana dalilin da ya sa kungiyar ta yanke shawarar cewa, babu wani zabi illa korar kocin da ya dade yana yi.
Pace ya ce: “Da farko, muna so mu sanya godiya ta gaske ga Sean da ma’aikatansa, saboda nasarorin da suka samu a kulob din cikin shekaru goma da suka gabata.