A ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Kigali, babban birnin kasar Rwanda, domin halartar taron kungiyar kasashe renon Ingila karo na 26 (CHOGM).
A cewar wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar, taron wanda zai gudana tsakanin 20 zuwa 26 ga watan Yunin 2022, zai mayar da hankali ne kan ci gaba da wadata na sama da mutane biliyan biyu da suka kunshi kasashen Commonwealth.
Sanarwar ta ce, a lokacin da yake Kigali, ana sa ran Buhari zai gabatar da jawabi kan babban taron cutar zazzabin cizon sauro da rashin kula da cututtuka na wurare masu zafi, da kuma tattaunawa da wasu shugabannin da suka halarci taron.