Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da ɗage kidayar jama’a da gidaje na shekarar 2023.
Buhari ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da ya yi da wasu mambobin majalisar zartarwa ta tarayya da kuma hukumar kidaya ta kasa a daren Juma’a.
Ya ce gwamnati mai zuwa ce za ta tantance kidayar da aka shirya tun daga ranar 3 zuwa 7 ga Mayu.
A wata sanarwa da ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya sanyawa hannu kuma ya fitar a ranar Asabar ta ce, “A lokacin da ya isa wurin yanke shawarar dage kidayar jama’a, taron ya sake nanata muhimmancin gudanar da kidayar jama’a da gidaje, shekaru 17 da yin hakan. Ƙididdiga ta ƙarshe, don tattara bayanai na zamani waɗanda za su fitar da manufofin ci gaban ƙasar da inganta rayuwar al’ummar Nijeriya.”
Ya ce Buhari ya lura da cewa, bayan kammala aikin tantance yankin da kasar nan ke yi, da gudanar da jarabawar farko da ta biyu, daukar ma’aikata da horar da ma’aikatan wucin gadi, da sayan na’urorin dijital na zamani (PDAs) da kayayyakin more rayuwa na ICT, an samu ci gaba mai gamsarwa a cikin aiwatar da ƙidayar yawan jama’a da gidaje na 2023.
Ya kuma yaba wa tsarin da hukumar ke bi, domin gudanar da sahihin kidayar jama’a, musamman yadda aka yi amfani da dimbin fasahar da za ta iya samar da kidayar jama’a a duniya da kuma kafa tushe mai dorewa na kidayar jama’a a nan gaba.
Buhari ya kuma umurci hukumar da ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da kidayar jama’a da gidaje na shekarar 2023, domin ci gaba da samun nasarorin da aka samu da kuma samar da ginshiki ga gwamnatin da ke kan gaba wajen karfafa wadannan nasarori.