Mukaddashin gwamnan jihar Kano, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a ranar Litinin din da ta gabata ya yi watsi da murabus din Manajan Daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA), Baffa Babba Dan-agundi. Dan-agundi ya rubuta kuma ya mika wa mukaddashin gwamnan takardar murabus dinsa a yau, amma gwamnan da ke hutu a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ya umurci mukaddashin gwamnan da ya ki amincewa da takardar.
Dan-agundi ya rubuta kuma ya mika wa mukaddashin gwamnan takardar murabus dinsa a yau, amma gwamnan da ke hutu a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ya umurci mukaddashin gwamnan da ya ki amincewa da takardar.
Da yake magana da Solacebase kan batun, Manajan Daraktan KAROTA, Baffa Babba Dan-agundi ya tabbatar da ci gaba da kin amincewa da murabus din da gwamnan yayi.
“Kun ga gwamna ba ubangidana ne kawai ba, amma kamar uba ne a gare ni, don haka sai in dauki duk abin da ya gaya mani,” in ji Baffa ga Solacebase.
‘’Gwamna Ganduje shi ne ya ba ni wannan mukamin na Manajan Darakta wanda ya inganta min matsayi a siyasance.
“A gaskiya, ba zan saba wa duk hukuncin da gwamnan ya yanke kan murabus na ba saboda ya san mafi alheri a gare ni,” in ji Baffa.
Da Solacebase ta tambaye shi dalilin yin murabus din Baffa ya ce, ”a gaskiya ina so in ci gaba da burina na siyasa na tsayawa takara amma duk sai na jira matakin da gwamna zai dauka.