Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya nada Sanata Dino Melaye a matsayin kakakin yakin neman zaben sa na shugaban kasa.
A wata sanarwa da mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe ya sanyawa hannu, an bayyana sunan Melaye tare da Dr. Daniel Bwala.
“Nade-naden biyu sun fara aiki nan take,” in ji Ibe a wata sanarwa.
Melaye ya kasance dan majalisar dattawa ta 8, wanda ya wakilci mazabar Kogi ta Yamma. Ya fito daga Ayetoro Gbede da ke karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi.
Bwala, a daya bangaren, kwararre ne a fannin shari’a, dan siyasa kuma manazarci harkokin jama’a. Ya fito daga jihar Adamawa.
Bwala, wanda har zuwa kwanan nan ya kasance jigo a jam’iyyar APC mai mulki, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, saboda tikitin takarar Musulmi da Musulmi na tsohuwar jam’iyyarsa.


