Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta kaddamar da kwamitocin tantance ‘yan takarar majalisar wakilai, dattijai da na jam’iyya mai mulki da za a tantance a yau da karfe 12 na rana.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakataren kungiyar na kasa, Sulaiman Argungu ya fitar.
A cewar Argungu, za a kaddamar da kwamitin tantancewar ne a Fraser Suites, Abuja.
Ya kuma bayyana cewa, daga nan ne za a fara tantance masu neman kujerar gwamna, majalisar wakilai da kuma ‘yan majalisar dattawa.
Argungu ya ce, za a gudanar da tantance ‘yan takarar majalisar wakilai a ranar Asabar 14 ga Mayu, 2022 a otal din Zeus Paradise, Abuja da karfe 2 na rana.
Ya bayyana cewa, za a gudanar da tantance masu neman takarar Sanata da Gwamna a ranar 15 ga Mayu, 2022 a Fraser Suites, Abuja ranar Lahadi, da karfe 10 na safe.