fidelitybank

DA ƊUMI-ƊUMI: APC ta rantsar da shugabannin jam’iya na jihohi 34 

Date:

 

Yayin da Jam’iyyar APC ke tunkarar babban taron ta na ƙasa a ranar 26 ga Febrairu, Kwamitin Riƙo na Jam’iyar APC ya rantsar da shugabannin jam’iya na jihohi, inda ya rantsar da na jihohi 34 da Birnin Taraiya a yau Alhamis a Abuja.
Sai dai kuma kwamitin bai rantsar da shugabannin jam’iyyar na Jihohin Kano da Sokoto ba.
Matakin ƙin rantsar da shugabannin jam’iyar na Kano da Sokoto ba ya rasa nasaba da rikicin jam’iyyar a jihohi biyun.
Jerin sunayen shugabannin da kwamitin ya rantsar a yau din da PlatinumPost ta ga ni sun haɗa da, Kingsley Ononogbu (Abia), Alhaji Ibrahim Bilal (Adamawa),  Augustine Enefiok Ekanem (Akwa Ibom),  Basil Ejike (Anambra), Alhaji Babayo Aliyu Misau (Bauchi), Dakta Dennis Otiotio (Bayelsa), Mista Augustine Agada (Benue), Honorable Ali Bukar Dalori (Borno), da kuma Mista Alphonsus Orgar Eba. (Cross River).
Sauran sun haɗa da  Elder Omeni Sabotie(Delta), Stanley Okoro Emegha (Ebonyi), Kanal David Imuse Mai ritaya (Edo), Barista Omotosho Paul Ayodele (Ekiti), Chif Ogochukwu Agballah (Enugu), Mista Nitte K Amangal (Gombe), Dr Macdonald Ebere (Imo), Hon. Aminu Sani Gumel (Jigawa), Air Comadore Emmanuel Jekada (Rtd) (Kaduna), Alhaji Muhammed Sani (Katsina), Alhaji Abubakar Muhammed Kana (Kebbi) Honorable Abdullahi Bello (Kogi).
Sai kuma Prince Sunday Adeniran Fagbemi (Kwara), Hon. Cornelius Ojelabi (Lagos), Mista John D Mamman (Nasarawa), Hon. Haliru Zakari Jikantoro (Niger), Chif Yemi Sanusi (Ogun), Injiniya Ade Adetimehin (Ondo), Prince Adegboyega Famodun (Osun), Hon Isaac Omodewu (Oyo), Hon Rufus Bature (Plateau), Chif Emeka Bekee (Rivers). Hon Ibrahim Tukur El-Sudi (Taraba), Alhaji Muhammed A. Gadaka (Yobe), Alhaji Tukur Umar Danfulani (Zamfara) da Alhaji Abdulmalik Usman (ABuja).
Ƙarin bayani na nan gaba…

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp