An ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Jubrin Abubakar a matsayin zababben shugaban karamar hukumar Gwagwalada a zaben ƙananan hukumomin da a ka yi na Abuja ranar Asabar.
Abubakar wanda tsohon shugaban ƙaramar hukumar ne ya doke abokin hamayyarsa, Mohammed Kassim na jam’iyyar PDP.
Abubakar ya samu kuri’u 11,125 kuma jami’in zabe na INEC, ID Umar ya bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da a ka fafata.
Kassim na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 9,597.