A na tsaka da tantance Balarabe Lawan, Ministan da Bila Ahmed Tinubu ya miƙawa majalisa, ya yanke jiki ya faɗi.
Sai dai lokacin ne shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana a kawo masa ruwa da sukari, ya kuma bukaci likitan majalisa ya kawo masa ɗauki.
Hakazalika Akpabio, ya umarci manema labarai su kashe kyamarar su tare da ficewa daga harabar majalisar.
Balarabe Lawan ya na ɗaya daga cikin mutumin da ya maye gurbin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i wanda suka fito daga jiha ɗaya.