Rikici na kara fitowa a zauren majalisar dokokin jihar Ribas.
Hakan ya biyo bayan tsige Edison Ehie a matsayin shugaban majalisar a safiyar ranar Litinin.
‘Yan Majalisar 24 ne suka rattaba hannu kan tsige Ehie.
Ku tuna cewa an samu tashin gobara a majalisar dokokin jihar Ribas a daren Lahadi (da daddare) wanda ya shafi zauren majalisar.
Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan na iya nasaba da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da ake zargin an yi.