Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Rt.Hon. Ahmed Muhammed, an tsige shi daga muƙamin sa.
A zaman gaggawa da suka gudanar a harabar majalisar da ke Lokoja a ranar Juma’a, ‘yan majalisar sun zargi Ahmed Muhammed da wasu manyan jami’ai uku da aikata muguwar dabi’a da kuma amfani da mukamai ba bisa ka’ida ba.
A wani kudiri na gaggawa wanda Hon. Enema Paul, mamba mai wakiltar mazabar jihar (Dekina/Okura), ya ce, ‘yan majalisa 17 ne suka sanya hannu kan tsige Hon. Ahmed Mohammed da kuma dakatar da wasu manyan jami’ai uku a gidan.
Manyan hafsoshin uku da aka kora daga mukaminsu, daga bisani kuma aka dakatar da su a gidan, su ne Bello Hassan Balogun (shugaban masu rinjaye), Idris Ndako (Mataimakin shugaban masu rinjaye), da Hon. Edoko Moses Ododo (Cif Whip), bulaliyar majalisar.