Biyo bayan harin da aka kai a cocin St Francis Catholic dake garin Owo na jihar Ondo watannin baya, an samu nasarar cafke wasu ‘yan ta’adda biyu da ake zargin ‘yan kungiyar IS ne a yankin yammacin Afirka (ISWAP).
Idan ba a manta ba a ranar Talata ne gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu ya tabbatar da cewa an kama wasu ‘yan ta’adda kusan biyar da ke da alaka da harin a jihar.
Kwanaki biyu kacal bayan rahoton, babban rundunar sojin a ranar Alhamis ta bayyana cewa, an kama wasu karin ‘yan ta’adda biyu da suka kashe sama da masu ibada 40 a cocin a ranar 5 ga watan Yuni.
Sanarwar ta fito ne a wata sanarwa da Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Jimmy Akpor ya fitar.
Da yake bayyana bayanan wadanda ake zargin, Janar Akpor ya ce su ne: Al-Qasim Idris da Abdulhaleem Idris.
Ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne a Omialafara (Omulafa), karamar hukumar Ose, jihar Ondo, a ranar Talata ta hanyar hadin gwiwa da sojoji da hukumar tsaro ta farin kaya DSS suka yi.


