Rundunar yan sandan a jihar Katsina, ta tabbatar da haramcin hana hawa mashin a duka fadin jihar.
Hakan na zuwa watanni hudu bayan da gwamnatin jihar ta dage haramcin na wucin gadi, don sauƙaƙa wa al’umma gudanar da ibadar Azumin watan Ramadana.
KARANTA WANNAN: Shehu Sani ya mayar da martani a kan hana Achaba a Najeriya
Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda, SP Gambo Isah ya fitar, ta ce saka dokar ya zama dole lura da yadda a baya bayannan yan ta’adda ke amfani da mashunan wurin kai hare-hare.
“Ana jan hankalin al’umma cewa an dabbaka dokar hana hawan mashin daga karfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safen kowace rana.”
Sai dai sanarwar ta ƙara da cewa a jihohin da suka fi fama da hare-hare dokar za ta fara ne daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya dake fama da hare-haren yan bindiga, da suka addabin yankin, lamarin da ya hada da makwabtanta Kaduna da Zamfara. A cewar BBC.


