A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka shawarci mazauna jihar Kogi da su guji cin naman shanu na akalla mako guda, sakamakon mutuwar shanu 20 a Lokoja.
Gwamnatin jihar ta ce, akwai yiyuwar shanun sun sha guba a lokacin da suke kiwo.
Daraktan Kula da Dabbobi na Ma’aikatar Gona ta Kogi, Dakta Salau Tarawa ne ya ba da wannan shawarar a wani taron manema labarai.
Ya ce, tuni naman shanun ya kasance a kasuwannin Lokoja, amma an dawo da shi.
Ya ce, tuni aka kai wasu shanun zuwa kasuwannin garin Osara a karamar hukumar Adavi; zuwa Ajaokuta, zuwa Obajana, zuwa Kotonkarfe da Kakanda domin sayarwa ga jama’a.
Ya kuma ce, ma’aikatar tana hada kai da jami’an tsaro domin gurfanar da makiyayan a gaban kotu.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban sashen Agro Rangers na jihar Kogi na hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC), Bayode Emmanuel, ya ce, an gano shanun ne a Lokoja.
“Shanun sun fito ne daga bayan harabar sakatariyar jihar, inda suka je kiwo. Ba zato ba tsammani, sai suka fara nuna wani hali, suka yi kasala suka mutu cikin mintuna.
Emmanuel ya tabbatar da cewa hukumar NSCDC za ta binciki lamarin sosai,.domin sanin inda matattun shanun suka yi kiwo da kuma hana sayar da naman da suka kamu da cutar.