An fara ƙirga ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya bayan kammala jefa ƙuri’un a yau Asabar.
Tuni turawan zaɓe a rumfar zaɓe ta Irona 3 mazaɓa ta 11 suka fara ƙirga nasu ƙuri’un.
Tun da misalin ƙarfe 2:30 aka kammala zaɓen a wasu rumfunan zaɓe, inda masu kaɗa ƙuri’a ke zaɓar ɗaya daga cikin ‘yan takara 17 da ke fafatawa.