Muhammad Sani Abacha da sanyin safiyar Alhamis ne ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a Kano.
Babban dan marigayi shugaban kasa, Janar Sani Abacha ya doke ƴan takara shi kadai, Alhaji Jafar Sani Bello a hedikwatar jam’iyyar ta jiha dake Lugard Avenue, Nasarawa GRA, Kano.
A karshen zaben fidda gwanin da aka yi mai zafi, Barista Amina Garba, ta bayyana Alhaji Abacha a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 736 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Jafar Sani-Bello, wanda ya samu kuri’u 710.