Za a ɗan dau lokaci ana kidaya kuri’un ganin cewa daliget sama da 2,000 ne suka kaɗa wannan kuri’a daga jihohin Najeriya.
Kidaya kuri’un na tafiya lafiya kawo yanzu ba tare da wata matsala ba.
Yayin da ‘yan Najeriya suka zuba ido domin ganin yadda za ta kaya wajen fitar da ɗan takara tilo a jam’iyyar APC wanda zai gwabza da Atiku Abubakar na PDP.