Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajowa a majalisar tarayya, Honorabul Shina Abiola Peller, ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Peller wanda dan asalin garin Iseyin ne a shiyyar Oke Ogun geo-political zone a jihar Oyo, ya bayyana hakan ne ta wata wasika da ya aikewa shugaban gundumar sa.
An zabi Peller ne a jam’iyyar APC a 2019.
Ya kasance daya daga cikin masu neman kujerar Sanatan Oyo ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC a zaben fidda gwanin da aka yi kwanan nan.
Sai dai dan majalisar ya fice daga APC, amma bai bayyana inda ya koma ba.
Peller, a cikin wasikar da ya sanyawa hannu da kan sa kuma ya aika wa shugaban jam’iyyar APC Ward 9, Koso a karamar hukumar Iseyin, ya dage cewa ya dauki matakin ne bayan ya yi shawarwari da jama’ar sa.