Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar Juma’a sun kai harin bam a ofishin ‘yan sanda da ke Eika-Ohizenyi a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi, inda suka kashe wani sufeto Jibril da ke bakin aiki.
Wani mazaunin yankin, Malam Momoh Abubakar, ya bayyana cewa, maharan sun mamaye wajen ne da misalin karfe 12:15 na safe dauke da bama-bamai da sauran makamai.
Ya bayyana cewa, bam na farko da suka jefa a cikin ofishin ya yi wani kara mai karfi da ta tada da yawa mazauna wurin, inda ya kara da cewa , bama-baman da suka tayar da wani bangare na ofishin ‘yan sandan.
Abubakar ya kara da cewa, maharan sun samu ranar, domin sun shafe sama da sa’o’i biyu suna gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama daga jami’an tsaro ko jama’ar gari ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, Edward Egbuka, ya ce, ya ba da umarnin tura karin kadarorin aiki, wadanda suka hada da jami’an rundunar ‘yan sanda na sashin yaki da ta’addanci, sashin amsa gaggawa, ofishin leken asiri na jihar tare da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro don dawo da zaman lafiya yankin. In ji Daily Trust.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP William Aya, wani bangare na ofishin rundunar ‘yan sandan yankin ya kone kurmus da maharan suka yi amfani da su.