Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta ce, ta kashe wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a yayin wani artabu da bindiga a garin Benin a ranar Lahadi.
A cewar rundunar, ta samu labarin da sanyin safiyar Lahadi cewa, wasu gungun ‘yan fashi da makami sun kai farmaki kan wani ofishin mai da ke kan hanyar Murtala Mohamed, a cikin garin Benin, inda nan take kwamandan Crack Team ya tattara tawagar ‘yan sanda da ‘yan banga zuwa wurin.
Daga baya an samu nasarar bibiyar ‘yan fashin zuwa wani wuri na daban inda ake zargin sun sake kai wani harin na fashi da makami.
Da ganin tawagar jami’an tsaro, an ce ‘yan fashin sun bude musu wuta wanda ya kai ga yin artabu da bindiga.