fidelitybank

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan sanda sun murƙushe ƴan IPOB a wani artabu

Date:

Rahotanni sun tabbatar da cewa, an kashe wasu da ake zargin ƴan kungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra IPOB, a wani artabu da ‘yan a garin Omuma, mahaifar gwamna Hope Uzodimma da sanyin safiyar Lahadi.

An kashe ‘yan bindigar ne bayan sun kai hari ofishin ƴan sandan Omuma da ke karamar hukumar Oru ta Gabas a jihar Imo, kamar yadda CSP Mike Abattam, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Imo ya bayyana.

Ya ce, ƴan bindigar sun buɗe wuta bayan sun abka ofishin ƴan sanda da safe, amma a cewarsa ƴan sanda sun murƙushe su a musayar wuta.

Jami’in ya ce, mutum huɗu aka kashe yayin da wasu saura suka tsere cikin daji raunuka a jikinsu.

Wannan na zuwa ne bayan wasu ƴan bindiga sun kai hari ofishin ƴan sanda a Umuguma da ke yankin Owerri ta Yamma tare da kashe ƴan sanda biyu a ranar Asabar.

Haka kuma ƴan bindigar sun kai hari gidan shugaban ƴan ƙabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo inda suka ƙone gidansa a jiya Asabar.

legit.ng.news.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp