Jami’an tsaro a jihar Zamfara, sun ceto mutum 14 daga hannun ‘yan bindiga a garuruwan Nasarawar Wanke da Rijiya da ke karamar hukumar mulkin Gusau.
A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na Rundunar Yan sanda a jihar, SP Mohammed Shehu ya fitar, ya ce, an kubutar da mutanen ne a dajin Kuncin Kalgo, kuma sun hada da mata 10, da maza biyu, da jarirai biyu.
SP Muhammad Shehu ya ce, sun samu bayanan sirri kan inda aka boye mutanen, kuma aikin ceton na hadaka ne da wasu yan kishin jiha da ke son ganin an samu zaman lafiya a Zamfara.
Tuni an mika mutanen ga yan uwansu, bayan jawabin manema labarai a shelkwatar rundunar da ke Gusau.


 

 
 