Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders’ Association of Nigeria (MACBAN), Adamu Aliyu a unguwar Gwagwalada da ke Abuja.
An kashe Aliyu ne tare da wasu mutane hudu a kusa da kauyen Daku da ke gundumar Dobi ta karamar hukumar a ranar Alhamis.
Mohammed Usman, Sakataren MACBAN, yayin da yake tabbatar da kisan shugaban, a ranar Lahadi ya ce, an kuma yi garkuwa da mutane uku.
A cewar Usman, wasu uku sun jikkata kuma an kai su asibiti. Ya ce, marigayi shugaban MACBAN da wasu mutane shida suna dawowa ne daga Kasuwar Izom ta Jihar Neja, lokacin da aka kai masa hari.
“Suna dawowa daga Kasuwar Izom da ke Jihar Neja inda suka je sayar da shanu, sai da ya kai kilomita daya kacal zuwa kauyen Daku, kwatsam ‘yan fashin sun fito daga daji suka bude wa motar wuta, inda suka kashe shugaban MACBAN da wasu hudu,” inji shi. .
Ya bayyana sunayen wadanda aka kashen a matsayin Saleh, Aliyu, Muhammadu da Saidu, yana mai cewa an binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Ya ce, jami’an tsaro suna nan a wurin kafin a yi jana’izar marigayin.
Shima shugaban karamar hukumar Gwagwalada Alhaji Adamu Mustapha ya tabbatar da faruwar lamarin.