Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane biyar da suka hada da ‘yan sanda biyu, malamin jami’a daya da kuma wasu biyu a wasu hare-hare a jihar Benue.
DAILY POST ta tattaro cewa, an kai hare-haren ne a kananan hukumomin Guma da Ukum na jihar.
An kashe ‘yan sanda kusan biyu a Yelewata da ke karamar hukumar Guma, da ke kan iyaka tsakanin jihar Binuwai da Nasarawa a lokacin da ‘yan bindigar suka far wa yankin.
Hakazalika, an kashe wani mai suna Fred Akaayar, malami a sashin sadarwa na jami’ar tarayya dake Wukari a jihar Taraba da wasu mutane biyu a Jootar dake karamar hukumar Ukum, dake kan iyaka tsakanin jihohin Benue da Taraba a daren ranar Alhamis.