Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Mada da ke karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Rahotanni sun ce, ‘yan bindigar sun kashe mutum daya tare da yin awon gaba da wasu shida.
An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun kai farmaki gundumar Mada da ke Gusau, babban birnin jihar, inda suka fara harbe-harbe ba da jimawa ba, lamarin da ya sa kowa ya gudu.
A cewar wani Abubakar Mada da ya zanta da DailyPost, akwai ofishin ‘yan sanda a gundumar Mada amma babu wani abin da suke yi na tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar gundumar.
Ya ce, “Jami’an ‘yan sanda a can ba su da bindiga don kare kai balle su kare wani mutum. In ji Independent.