Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a safiyar ranar Litinin, sun mamaye harabar gidan rediyon Anambra (ABS), da ke Awada, a tashar Onitsha.
‘Yan bindigar da ake kyautata zaton cewa suna cikin wadanda ke addabar jihar sama da shekara guda, sun kona wani gini da motar bas na tashar, da wata mota da aka ajiye a harabar ta wani ma’aikacin da ya yi aikin dare daya.
DAILY POST ta rawaito cewa, ba a samu asarar rai ba a harin, amma ‘yan bindigar sun musgunawa ma’aikatan da suka hadu da su a harabar, inda suka yi musu rauni.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, wani ma’aikaci da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce jami’an tsaro na yi musu tambayoyi kan harin.
Ya yi alkawarin ba da cikakken bayani kan harin da ‘yan bindigar suka kai musu, kamar yadda ya kwashe dare yana aiki, kuma ya shaida harin.