Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta yi barazanar hargitsa shirin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulki da jam’iyyar adawa ta PDP “sai dai idan ba a bude jami’o’in Najeriya a halin yanzu da ke kulle da makullan ba.
Wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi mai dauke da sa hannun shugabanta, Sunday Asefon, NANS, ta yi Allah-wadai da gaggawar neman tikitin jam’iyyar da ‘yan siyasa ke yi yayin da jami’o’in suka rufe kusan watanni uku.
Asefon ya bayyana ‘yan siyasar Najeriya a matsayin “masu sani, miyagu, masu son kai da kuma rashin mutunci.”
Ya ce, abin takaici ne yadda ‘yan jami’o’in Najeriya suka shafe kusan watanni uku ana hukunta su a gida, amma wadanda ke da alhakin tabbatar da ingancin karatunsu da ingantaccen ilimi suna da hurumin karbar fam Naira miliyan 100.