Sakataren kwamitin rikon kwarya na kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Sanata John James Akpanudoedehe ya yi murabus daga mukaminsa na jam’iyyar sa’o’i kadan bayan babban taronta na musamman da kuma zaben fidda gwani na shugaban kasa.
Akpanudoedehe ya sanar da matakin nasa ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 4 ga watan Yuni, 2022 kuma ya aikewa da shugaban jam’iyyar APC reshen Offot Ward 6, Uyo a jihar Akwa Ibom.
Wasikar mai take; ‘Sabuwar zamana na jam’iyyar All Progressives Congress’ ya ce; “Na rubuta ne domin sanar da ku cewa, na fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), nan take.