fidelitybank

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji sun kama ƙasurguman masu fashin daji

Date:

Rundunar sojan Najeriya, ta ce, ta yi nasarar kama ƙasurguman ‘yan fashin daji bakwai da masu taimaka musu a jihohin Kaduna da Filato da Nasarawa da ke arewacin ƙasar.

Wata sanarwa da Manjo Janar Benard Onyeuko ya sanya wa hannu ranar Juma’a ta ce dakarun rundunar sun yi nasarar ce cikin mako guda ta hanyar aikin haɗin gwiwa da mutanen gari da kuma bayanan sirri.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai Danladi Selfa mai shekara 23 da Usman Yau mai 28 a Ƙaramar Hukumar Logo ta Jihar Nasarawa bayan an raunata su sakamakon fafatawar da suka yi da dakaru.

Haka nan, an kama Moses Aindigh mai shekara 27 da IIiyasu Mohammed mai 37, su ma a Nasarawa.

A cewar rundunar, a ranar 3 da 4 ga watan Agusta aka kama ƙasurguman ‘yan fashi – Umar Zakari, Usman Hamina, Haruna Umaru a ƙauyen Fuskar Mata da ke Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Kaduna.

Dakarun sun kuma yi nasarar kashe Umar Mohammed da ake zargi da garkuwa da mutane a Ƙaramar Hukumar Qua’anpan ta Jihar Filato a ranar 3 ga Agsuta.

Har wa yau, sojojin sun kuɓutar da Ebuka Nnadi mai shekara 30 da kuma Uchenna Edoga mai 25, waɗanda aka yi garkuwa da su a Gindiri na Ƙaramar Hukumar Mangu ta Filato ɗin.

legitnewsnigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp