Dakarun soji na Brigade 13 da ke aiki karkashin runduna ta 82, sun tare wata mota makare da alburusai iri-iri a kan hanyar kauyen Utanga zuwa tsaunin Obudu a jihar Kuros Riba.
Birgediya Janar na hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jihar Enugu ranar Laraba.
Ya ce “Dakarun da aka tura a tura Operating Base Amana sun yi yunkurin tsayar da motar a shingen binciken su amma direban ya kaucewa binciken sannan ya zura ido. Direbobin sun jajirce
ya tilastawa sojojin bude wuta kan tayoyin motar, inda suka yi waje da ita.