Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Municipal, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya fita daga APC zuwa jam’iyyar ADP.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro bayanan cewa dan majalisar ya sami tikitin takarar gwamna a jam’iyyar ta ADP bayan komawar sa.
Rahotan ni sun bayyana cewa, Sha’aban din zai yi takarar ne tare da Rabiu Bako, a matsayin wanda zai masa mataimaki.
Wani makusancin Sha’aban, wanda baya so a bayyana sunan sa ya tabbatarwa da Solacebase cewa, dan majalisar zai bayyana fitar tasa dashi da magoya bayan sa kafin karshen wannan mako.