fidelitybank

Da Ɗumi-Ɗumi: Rundunar ƴan tsanda ta haramtawa jami’an ta sanya kayan gida

Date:

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da haramta sanya tufafin da ba a amince da shi ba ga jami’an ta, domin gudanar da ayyuka na yau da kullum.

Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta wallafa a yammacin ranar Juma’a.

Ya kuma umarci rundunar ‘yan sanda X-Squad da jami’an sa ido, domin tabbatar da aiwatar da umarnin.

Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya bayyana takaicin sa kan yadda jami’an ‘yan sandan da ke sintiri da masu gadi da tsayawa da bincike da sauran ayyukan ‘yan sanda suka saba wa ka’idar sanya rigar da aka amince da ita a Najeriya.

Ya kara da cewa, a yayin sintiri, jami’an ‘yan sanda sun samu dabi’ar sanya rigar gida da huluna musamman ma, “Jami’ai na musamman, Commando da MOPOL da kuma SCORPION da sauran su yayin da suke bakin aiki”.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa, ta bayar da umarnin cewa, dukkan sassan ’yan sanda musamman na Force Provost Marshal, IGP X-Squad da Monitoring Unit da su tabbatar da aiwatar da tsauraran umarnin tare da sanya takunkumi mai tsanani ga jami’an da suka yi karya doka.

“Dukkan jami’an sa ido za su fuskanci hukunci mai tsanani idan har jami’an da ke karkashinsu suka karya wannan umarni,” in ji shi.

thisday newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp