A yau ne kwamitin zartaswar jam’iyyar PDP na kasa zai yanke shawara kan raba tikitin takarar shugaban kasa gabanin babban zaben 2023 da ake sa ran zai yi.
Daily Independent ta tattaro cewa, za a gudanar da taron ne a yau Laraba a shelkwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.
Batutuwan da za a tattauna a wajen taron dai su ne batun raba yankin bayan da kwamitin mutane 37 karkashin jagorancin gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya mika rahotonsa ga kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC).