Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta ce, ta kama wasu mutane takwas da ake zargi da yunkurin damfarar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari dala biliyan biyu.
Wadanda ake zargin, a cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Talata, an kama wadanda ake zargin ne da yunkurin damfarar gwamnatin Buhari da ta kai dala biliyan biyu.
Jami’in ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa kama shi ya biyo bayan korafin da rundunar ‘yan sandan ta samu a ranar 25 ga watan Afrilu, ta hanyar koke daga Richard David, wakilin al’ummar Okpella, a karamar hukumar Etsako ta tsakiya a Edo.
Dan sandan ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun bayyana ne a ranar 14 ga watan Yulin 2021 a gaban mai karar da ‘yan uwansa, inda suka shaida musu cewa sun samu amincewa daga gwamnatin tarayya, ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF)., don kwashe kayan aikin bututun rijiyoyin burtsatse na dala biliyan biyu. In ji People Gazette.