Majalisar dokokin jihar Ribas, ta fara shirin tsige gwamnan jihar, Siminialayi Fubara.
Don haka, ‘yan majalisar dokokin jihar sun ba da sanarwar tsige Fubara bayan tsige shugaban majalisar, Edison Ehie, wanda ake kyautata zaton yana bangaren Gwamna.
Mambobi 24 cikin 32 na Majalisar Ribas sun sanya hannu kan takardar tsige Fubara.
An dai dauki matakin ne a zaman gaggawa da ‘yan majalisar suka yi a safiyar ranar Litinin.
Zaman da ba a saba gani ba ya gudana tsakanin karfe 7 na safe zuwa karfe 9 na safiyar ranar Litinin.