Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, ta wanke tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi takarar shugaban kasa a 2023.
Kotun ta yanke hukuncin ne a jajibirin zaben shugaban kasa na jam’iyya mai mulki.
Ana alakanta Jonathan da takarar Shugaban kasa a APC yayin da wata kungiya ta siya masa fom din Naira miliyan 100.
Sai dai kuma an sha samun matsaya daban-daban kan cancantarsa a zaben shugaban kasa na 2023.
Sai dai a ranar Juma’a, kotun ta ce, Jonathan, wanda ya sha kaye a zaben 2015 a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai iya tsayawa takara mafi girma a zaɓen.