Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya taya Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP), da Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress murnar fitowa takarar shugaban kasa a 2023.
Jonathan, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ikechukwu Eze, ya fitar ranar Alhamis a Abuja, ya kuma taya daukacin sauran masu rike da tutar shugaban kasar na sauran jam’iyyun da suka fito daga zaben fidda gwani na jam’iyyu daban-daban da aka kammala.
Wadannan a cewar Jonathan sun hada da Sen. Rabiu Kwankwaso na New Nigeria Peoples Party (NNPP), Malik Ado-Ibrahim na Young Progressives Party (YPP).
Cif Dan Nwanyanwu na Zenith Labour Party (ZLP), Dumebi Kachikwu na African Democratic Congress (ADC) da kuma Adewole Adebayo na Social Democratic Party (SDP).
Sai dai ya bukaci ‘yan takarar da su gudanar da yakin neman zabe ba tare da nuna kyama da rarrabuwar kawuna ba, ta hanyar tabbatar da cewa, al’amuran da suka tunkare Najeriya da ingantattun hanyoyin da za a bi wajen ganin sun shiga tsakani a yakin neman zabensu.
Ya bukace su da su guji tashin hankali da ayyukan da za su karfafa duk wani nau’i na zubar da jini.
Jonathan ya ce, fitowar su a matsayin masu rike da tuta a jam’iyyunsu bayan sun mika kansu ga zabuka masu tsauri da tsarin zabe ya nuna imaninsu da muradunsu ga ci gaban al’umma.