fidelitybank

Da Ɗumi-Ɗumi: Jami’in Birtaniya sun tsare Peter Obi

Date:

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, ya ce, jami’ai sun tsare tare da hantarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi a birnin London.

Mai magana da yawun kwamitin kamfe na jam’iyyar LP, Diran Onifade ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce, lamarin ya faru ne a filin jirgin sama na Heathrow da ke London.

Ta ƙara da cewa jami’an shige da fice na Birtaniya ɗin ne suka titsiye tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa.

Karanta Wannan: Ɗan takarar mu Obi ake hari ba jam’iyyar mu ba – LP

Diran Onafide ya ce, hukumomi a Birtaniya sun tsare tare da yin tambayoyi ga tsohon gwamnan na jihar Anambra kan wani lamari da ya shafi wani mutum da ke yin sojan-gona da suna Peter Obi.

Sanarwar ta ƙara da cewa, jami’an sun sassauta wa Petetr Obi ne bayan wasu ƴan Najeriya da ke a filin jirgin sun sanya baki.

Peter Obi dai ya isa birnin na London ne, domin bukukuwan Easter na mabiya addinin Kirista.

Bayanin ya nuna cewa, bayan saukar Peter Obi a filin jirgin na Heathrow da ke London, jami’an tsaro sun zo wurin sa a lokacin da yake kan layin tantancewa, tare da miƙa masa wata takarda da ke ƙunshe da umurnin tsarewa, sannan suka buƙace shi da ya fita daga layi.

Onifande ya ce, jami’an sun yi wa Peter Obi tambayoyi na tsawon lokaci, wanda abu ne da ba a saba ganin ya faru ga wani mutum da ya kwashe sama da shekara 10 yana rayuwa a ƙasar ba.

Sai dai mutane ƴan asalin Najeriya sun rinƙa ɗaga muryoyinsu, domin sanin dalilin da ya sa aka tsare tsohon gwamnan.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...
X whatsapp