A yammacin ranar Talata ne gwamnonin jam’iyyar PDP suka hallara a Abuja domin wani taron gaggawa.
An tattaro cewa an kira taron ne kan rikicin da ke faruwa a jihar Ribas, inda wasu ‘yan majalisar dokokin jihar suka fara yunkurin tsige Sim Fubara, gwamnan da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP.
Yanzu haka dai gwamnonin PDP na can a masaukin gwamnonin jihar Oyo da ke Abuja domin taron gaggawa.
Wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas sun yi yunkurin tsige Fubara tsakanin daren Lahadi zuwa safiyar Litinin.
Wasu daga cikin gwamnonin PDP da ake ganin za su iso sun hada da Fubara, Bala Mohammed, Bauchi, Caleb Muftwang, Plateau, Dauda Lawal, Zamfara, da Ahmadu Fintiri, Adamawa.
Sauran sun hada da Ademola Adeleke na Osun, Agbu Kefas, Taraba, Godwin Obaseki, Edo da Sheriff Oborevwori, Delta.
Mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa karkashin jagorancin shugaban riko, Iliya Damagum, sun isa wurin taron.