fidelitybank

Da Ɗumi Ɗumi: Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24

Date:

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura tare da fara aiki nan take biyo bayan shawarwarin da jami’an tsaro suka bayar, bayan wani hari da wasu da ake kyautata zaton Fulani ne suka kai wa yankin Agban Kagoro da kewaye wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.

Sanarwar da Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar ta bayyana cewa, “Bayan shawarwarin da hukumomin tsaro suka bayar, gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura tare da fara aiki nan take. Hakan na nufin taimaka wa jami’an tsaro wajen daidaita al’amura a yankunan, da ceton rayuka da dukiyoyi da kuma ba da damar maido da doka da oda.”
Sanarwar ta kuma bayyana cewa hukumomin tsaro na da cikakken ikon aiwatar da dokar hana fita.

Gwamnati ta yi kira ga daukacin mazauna kananan hukumomin Jema’a da Kaura da su ba jami’an tsaro hadin kai a aikin gaggawa na maido da zaman lafiya da bin doka da oda.

Sai dai gwamnatin, a cewar sanarwar, ta yi Allah-wadai da tashe-tashen hankula da duk wasu ayyukan rashin bin doka da ya afku a yankin.

vgn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp